DOWNLOAD BURIN RAINA EPISODE 1
A kwai wani labarin soyayya mai dadi daza kuji tsakanin salim da salima dakuma najib, ina zakuji alhaji mahmud baitaba
samun haihuwa ba sama da shakera ashirin, amma yana da yaro kwaya daya tak shikadai Allah yabasu, kuma shi alhaji mahmud mai kudi ne sosai yana da kanfanunuwa daya masu tarin kudi sannan yana da kadarori masu yawa, sai kuma wannan yaro nashi daya tak ya daukeshi ya kaishi kasar waje karatau, bayan yaron yasami wata cuta mai suna blood cancer kenan, ana cikin haka sai najib yadamu da yadawo gida kusa da iyayensa saboda likitansa acan yace saura wata shida kacal yaregemasa, a wani bangare kuma zakuji inda alhaji mahmud yake ta shirya gida saboda dansa najib zai dawo nigeria sai yafito daga falo yaji kida yana tashi sai yace kai salihu sai yakira har sau uku bai amsa ba sai yakira mai talaja sai yace kiramin salihu shikuma dama baya ji sosai sai ya kwankwasa masa gilas sai
DOMIN SAUKE BURIN RAINA EP.1 DANNA
yabude mota yace alhaji yana kiranka yace to, alhaji muhmud yace ku goge ko ina acikin gidannan saboda yau najib zai dawo daga Qatar yau ina cikin farin ciki sosai, sai alhaji mahmud yace kashirya mota zakaje airport ka daukoshi amma fa kacanza wannan kayan sai salihu yace to alhaji, sai alhaji mahmud yace idan kundawo kuma kuna da tukwuici mai tsoka sai mai talaja yace da salihu alhaji yace zai bamu kudi idan mundawo yace shikenan, ana cikin haka sai sukaje suka daukoshi sai suna tafiya yanacewa ai garin namu ya canza gabadaya naga wani iri garin yake sai salihu yace kash danma daga kasar waje kake wadansu idan sunzo sai suce kamar wani kasar waje garin saboda suna ganin yamusu kyau sosai, sai suka isa gida dama yakira salim yace masa gashinan yashigo gari fa amma yanzu haka yana hanya zuwa gida, sai salim yace Nima yanzu zanzo gidan ina studio ne ina karasa wani aiki amma yamzu zanzo, sai najib ya isa gida sai mamansa ta fito da babansa suna masa oyoyo oyoyo tare da yan aikin gida, ashe tun lokacin dama bashi da lafiya amma bai gayama ummansa ba sai yaboye mata, shima alhaji mahmud baisani ba har sai da doctor yagaya masa sannan yasani, amma duk dahaka babansa bai yarda ba saboda bashi da wani yaro wanda yawuce najib shikadai Allah yabasu, a gurin da alhaji mahmud zai gane dansa bashi da lafiya ya daukeshi yaje dashi wajen company nashi inda ake ta renovation nasu saboda yanaso ya mallakawa najib sai yaga jini yana fita ta hancinsa sai yace masa miye wannan sai yace bakomai ashe shi najib yasani dama sai alhaji mahmud yace muje muga doctor gaskiya, sai da sukaje sai doctor yace masa yana da blood cancer sai alhaji mahmud yace dan nawa daya tal shine yake dauke da wannan cutar sai jikinsa yayi sanyi sai alhaji mahmud yace yanzu doctor babu yanda zamuyi sai yace gaskiya babu yanzu haka wata shida ne yarage masa a duniya, sai alhaji mahmud yace gashi ko jikana bangani ba amma Allah zai karbi Kayansa, sai doctor yace amma ina da wata shawara guda daya, zan taimaka maka kamar yadda kuma kuke taimakawa, amma kuma sai dai akwai matsala daya tak ok babu damuwa, sai doctor yace mai zai hana najib yazo yasami yarinya ta ya aura shine abin da zaifi sauki, sai alhaji mahmud yace kwarai doctor amma naji dadin haka sosai, sai doctor yace amma akwai wani alkawari daya dana dauka shine bazan yiwa 'ya ta auren dole ba ko wanda bata so amma najib yaje yasameta su fahinci juna idan ta amince to shikenan nima na amince,sai alhaji mahmud yaji dadin haka sai yaje yasamu najib yagayamasa ya samomai mata yashirya yaje yaganta, sai yace to shikenan baba zan shirya yanzu ko sai gobe yace ko yaushe ma kashirya yace shikenan to yau zamuje, sai yaje yasami salim yace abokina da matsala fa dady yace naje nashirya yasamomin matar aure fa wai zamuje na ganta sai salim yace wannan ba matsala bace ai kasan dai yan matan nigeria sai kaje musu da karya zasu soka idan kaje da gaskiya bazasu soka ba amma kuma wannan dogayan kaya sai ka ciresu kasa kananu fa saboda suna son gaye sosai kasha kananu kaya shine birgewa a wajensu, sai najib yace taya zan koyi sa wannan kaya sai salim yace a hankali zaka koya wallahi kadai kayi hakuri na kwana kadan zakaji dadinsu sosai, sai najib da babansa sukaje gidan doctor sai suka zauna suna fira sai hajiya ma ta zauna sai doctor yace ina wannan yarinya sai hajiya tace tana ciki sai yace kirata mana tazo su gaisa sai tace to sai aka Kira salima sai ta gaidasu gabadaynsu sai sukace bara suje suyi magana a waje sai suka bar salima da najib.