DOWNLOAD HAUSA SERIES
hausazone.com.ng

Home
Music
Videos
Kanny
👉 LATEST DAILY HAUSA SERIES UPDATES 👈

LABARINA EP 26

DOWNLOAD LABARINA EP 26




A satin da ya wuce mun tsaya a daidai inda Mahaifin Laila ya kira ta ya sanar da ita cewa Mahmud bashi da uba wato dan shege ne.

Toh a wannan satin kuma lailai taje tasamu kawayenta ta fada musu duk yadda sukai da Dady ta akan Mahmud.

Babban abokin Mahmud wato Umar yaxo yana cewa yaga Sumayya ta zama mawakiya 😂😂😂. Shi kuma Mahmud yace ai yaje wajan Ali jita yace mai ai ko baka da murya zaka iyya yin waka ba komai, sai shikuma abokin sa yace toh yanxu inzai waka wani sako zai fada aciki bayan shi da aka bashi amana yaci. Nan take ran Mahmud ya baci.

Kawar Sumayya kuma take bata shawara take ce mata tunda dai Mahmud sun rabo toh yakamata tabawa Lukman dama ya taka rawar kalar Soyyayar da yake mata. Uhm su sumayya manyan mawaka wai ta cikin waka takeson sanar mai da tata soyyar hakan kuma akayi.

Amma  ta hadu da sharin yaran abroad wato yar uwar 


Domin Sauke Kashi na 26 Danna 
Lukman da ke karatu a kasashen turai wai itama ma ta dage da son Lukman. Ga kuma Mom nashi tasashi agaba sai anyi hadin gida amma abari tukunna su da saba sosai kafin a fara maganar auren su.

Lukman kuma yaji mugun dadin yadda sumayya ta fada masa yanxu tana sonsa sosai, Saboda Tsabar jin dadi harda zuwa wajan ta. Saboda zakewa har ya sanar da Mom nashi sannan wai za ai Auren nan bada dadewa ba.

Toh fa ga Mahmud ga Laila koya zata kasan ce dan naga Laila fa yau rai ya baci.
Domin taje taje tayi bin cike tsakanin Mahmud da Sumayya an kwashe tatas an fada mata. Sannan yanxu tacewa Mahmud face -face kai fa ba dan halak bane domin baka da Uba wato Mahaifi kai dan shege ne in kuma ba haka bane toh ka musanta inajin ka.

Subahanallah Mahmud fa na tsaka mai wuya domin ni kai na ya ban tausayi😭😰😋😂.
Allah sarki ya kama hanya ya tafi gida ya samu Mamar shi yake tambaya wai bata hanyar Halal aka haifeshi ba yace Dan ALLAH ta fada masa Gaskiya don baya tayi abun kunya yanxu kam kar asake hakan shine sai ta fadama masa, Alokacin da batajin magana ne hakan ya faru.
Shine babban dalilin yasa taake son a hada auren sa da Murja saboda idan za'ai Auren shi da Murja baza ai wani dogon bincike ba. Ballentana azo kan abunan har a gane. Toh masu kallo anan Na 26 ya kare.

Toh Allah ya basu ikon cigaba .


Created And Designed By Arewafamily

Place adverts on the sections of HausaZone For your Daily Business Growth, Here