DOWNLOAD A DUNIYA KASHI NA 17
A satin daya gabata kunji inda canavaro yace cisco suyi da dukan wanda sukazo masa gida neman wayarsu da aka sace, sai suka fara duka ta ko ina suna kuka yana cewa waya turoku gidan sunce wani ne yace idan sunzo gidan zasu sami wayarsu sai yace kiyu ta dukansu har sai sunfadi wanda ya turoku gidana, sai canavaro yace gidana gidan sata ne dazaku zo kuce zaku sami kayanku.
A wannan satin kuma zakuga inda manyan unguwa suka zauna dasu da Mai unguwa kan cewa yakamata aje ayi magana da mai gidan kode yatashi yabar unguwa ko kuma musayi gidan bazai yu ba ace kullum sai maza da mata suna shiga kuma gashi bashi da mata idan yana so
yaci gaba da zama sai dai ya dauko matarsa da yaransa yakawo gidan sai alhaji ado yace shi zai iya siyan gidan sai suyi makarantar islamiyya kunga yara Sun sami sauki karatu ai sai alhaji garba yace shima zai iya siya amma idan haka bata kasance ba zasu je wajen sarki su kai kukansu kaga zai magance matsala ai, daga jin haka sai mai unguwa yace haba alhaji ado meyasa kake irin wannan magana wallahi ko dayaushe idan anzo ana sulhu sai ka kawo mana maganar shamaki wallahi zan tsinkeka da mari sai alhaji
Ado yace haba mai unguwa mai yayi zafi haka har da mari Sai, mai unguwa yace wallahi zamu bata kana kawo mana magana mai gari anan, sai malam yace akwai wata shawara daya kuma itace yakawo matarsa ya zauna acikin gidan kaga shikenan kowa yahuta ai, daga jin haka sai mai unguwa yace alhaji garba nifa wannan rawani ba ni na daurawa kaina ba nima bani akayi amma duk kabi kasa idanu akai, bayan haka sai suka yanke matsa kan mai unguwa zaije yasami canavaro suyi magana ta sulhu kan yadda mutanen unguwa suke magana akai, A wani bangare kuma zakuga inda alhaji yazo gidan malam wakataba domin yaji meyasa yar aikin gidansa bata zuwa sai yazo gidan yasameta suna zaune sai takawo masa abinci da ruwa tace yaci yace har namma sai kinyi girki amma yayi dadi har naji kanshinsa wallahi sai yace yawwa nakoshi yasha ruwa sai yace mata hajiya tazo gidan nan kuwa sai tace tazo sai yace mai hali baya fasa halinsa, nazaci bata zoba ai sai tace tazo har tabani 1000 daya ma yace ayya yanzu yaushe zaki koma gida kicigaba da aiki sai tace ai sai matar malam ta dawo wata yarinya Aka kawo shine ta bata sai iyayen ta zuka zo nemanta shine basu ganta ba sai suka tafi da ita shine nake musu girki nake bayarwa ake kaimata sai yace yayi kyau amma da zarar tadawo to kikoma gida muna jiranki sai yace zankoma yanzu ga shi yabata kyautar atamfa harda kudin dinki sai tayi godiya sosai ta rakashi yatafi, sai ga mutumin kauye yana zaune yana jiran dan sanda yafito yaji ansami wani cigaba kan batun yar sa sai gashi yazo yace ina ta nemanka sai yace ina kashiga ne sai yace amma ka kara hakuri yanzu haka oga yana waya yanaso aje a taho da waccan matar wacce ta dauki yarinyar ka yace Allah mungode maka insha Allah sai ankwato Min hakkin yarinya ta inanan babu inda zani sai yakira dansa yace yaje yakamo wani rago yakai kasuwa domin yasiyar yakawo musu kudin sai yace yabawa matarsa naira 1500 kacal kar yakara idan ansaida rago naira 15000 idan bai kai haka ba kar yasiyar yadawo dashi gida sai yace yaro yatafi gida wato kauye kenan.
Muhadu A kashi na gaba.
Created And Designed By Arewafamily