Download Dadin Kowa Wasa Farin Girki
A satin daya wuce adama takira yarta domin sakata wani aiki amma taki yi domin ko a wanne addini ne tasaba dokokin sa.
Toh a wannan satin kuma Masoyan nan wayo kamaye da Dillaliya suna shan soyyar su inda ita Dillaya ta dinkawa kamaye wasu sabbin manyan fararin kaya.
Domin Sauke Kashi na 63 Danna
A chan bangaren gidan tsohon soja kuma dayar matar sa take bashi shawara domin karya sake yafita daga gidan batare da ya lallashi Baraka ba bayan sun dan samu musayar yawu tace ba'a mata adalci a cikin gidan nan. Shi kuma Salihu kansila yazo wajan rabon kayan Government inda akai ta mishi kirari domin xai raba Injin murza taliya da kuma Injin nikah da sauransu, inda a kanawa kaka Wizzzy Tabawa keken dinki taita godiya harda kukanta kunsan kuka ba yawa tsoffafi wahalar yi. Chan saiga Alhaji Buba yazo yana siyan kayan da aka rabawa Mutanen har suka kusan samun matsala da kaka tabawa. Gidan Mallam Dalha >> yabawa yaronshi dubu biyu domin yaje mahauta yasiyo nama bujimi ya kaiwa Adama a boye sannan a sanar da ita yasha daddawa sannan kar ya sake yabar azumi ta gani.